Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan Bunƙasa Wasanni a Matakin Tushe, Hon. Adeyinka Anthony Adeboye, ya bayyana rashin isassun tsare-tsare da damammaki a matsayin babban ƙalubale ga ci gaban wasanni a matakin tushe a Najeriya.
Hakan na faruwa ne duk da yawan ƙwararrun matasa masu baiwa a fannin wasanni da ƙasar ke da su.
Adeboye ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake gabatar da jawabi a wajen buɗe taron ƙasa kan Bunƙasa Wasanni a Matakin Tushe na shekarar 2026 (2026 National Grassroots Sports Summit), wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
-
Tinubu ya buƙaci da a bunƙasa harkokin wasanni daga tushe
-
Real Madrid ta sanya Yuro miliyan 150 kan Vinícius
-
FIFA ta nada mambobi biyar a kwamitin rikon kwarya na NFF
Da yake magana kan taken taron mai taken, “Ƙirƙirar Sabuwar Hanya Domin Dorewar Bunƙasa Wasanni a Matakin Tushe a Najeriya,” ya yi kira da a samar da haɗin gwiwar ƙasa baki ɗaya, wanda zai haɗa da gwamnatocin jihohi, hukumomin ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin wasanni da kuma kamfanoni masu zaman kansu, domin gano matasa masu baiwa, da haɓaka ƙwarewarsu da kuma tallafa musu.
Adeboye ya ce: “Najeriya ba ta rasa ƙwararrun masu baiwa a fannin wasanni ba, amma abin da ta rasa shi ne isassun tsare-tsare da damammakin da za su taimaka wa matasa ‘yan wasa wajen cimma burinsu da amfani da baiwar da suke da ita.”
Ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su ƙara zuba jari a wasannin makarantu da na al’umma, da inganta kayayyakin more rayuwa na wasanni, da ƙarfafa tsarin gano matasa masu baiwa tare da samar da ƙarin damammaki ga matasa ‘yan wasa a faɗin ƙasar.
Haka kuma, Adeboye ya jaddada muhimmancin faɗaɗa shirin bunƙasa wasanni a matakin tushe zuwa dukkan ƙananan hukumomi 774 na Najeriya, yana mai cewa bai kamata a hana yara masu baiwa damar nuna ƙwarewarsu saboda inda suke zaune ko kuma matsayinsu na zamantakewa ba.
Baya ga samar da fitattun ‘yan wasa, ya bayyana bunƙasa wasanni a matakin tushe a matsayin wata muhimmiyar hanya ta bunƙasa tattalin arziki, wadda za ta iya samar da ayyukan yi, haɓaka harkokin yawon buɗe ido, da jawo masu zuba jari da kuma tallafa wa ci gaban al’umma.
Ya kuma ƙalubalanci mahalarta taron da su tabbatar da cewa taron na tsawon kwanaki biyu ya samar da sakamako na zahiri, yana mai jaddada cewa bai kamata a auna nasarar taron da yawan jawaban da aka gabatar kawai ba.
