Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buƙaci matasan yankin Kudu maso Kudu da sauran ’yan Najeriya su guji tashin hankalin zaɓe, amfani da su wajen maguɗin siyasa, yaɗa kalaman ƙiyayya da kuma bayanan ƙarya gabanin babban zaɓen 2027.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ƙungiyoyin matasa a yankin Kudu maso Kudu, wanda wani ɓangare ne na shirin da take gudanarwa a yankuna shida na ƙasar domin ƙarfafa zaman lafiya, sahihancin zaɓe da kuma shigar matasa cikin harkokin dimokuraɗiyya.

Kwamishinan Zaɓe na Jihar Akwa Ibom, Farfesa Anugbum Onuacha, ya yi kira ga matasa da sauran masu ruwa da tsaki da su taka rawa wajen tsara yadda za a gudanar da zaɓe, tare da jaddada muhimmancin gaskiya, ƙwarewa da kuma shigar da kowa cikin tsarin zaɓe.

Ya tabbatar da cewa INEC ba ta da jam’iyya ko ɗan takara, kuma tana amfani da darussan zaɓukan baya wajen inganta ayyukanta.

Haka kuma, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) sun buƙaci matasa su guji zama kayan aikin siyasa wajen haddasa tashin hankali, tare da amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa sahihan bayanai da wayar da kan jama’a.

Sun kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya, haƙuri da kuma balagar siyasa.

A yayin taron, jami’an INEC sun gabatar da bayanai kan shirye-shiryen zaɓen 2027, laifukan zaɓe da hukuncinsu, amfani da na’urorin BVAS da sabbin fasahohi, da kuma rawar da matasa za su taka wajen yaƙi da bayanan ƙarya.

An kuma ƙirƙiri ƙungiyar WhatsApp domin ci gaba da tattaunawa, wayar da kan matasa da kuma musayar ra’ayoyi tsakanin hukumar da wakilan ƙungiyoyin matasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *