Ƙungiyar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa, The Big Tent, ta buƙaci ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun hamayya su haɗa kai tare da samar da ɗan takara guda da zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na 16 ga Janairu, 2027.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyun adawa da su fara tattaunawa kan samar da tsarin gwamnati mai haɗa kowa, domin shirya wa yiwuwar karɓar mulki bayan zaɓen.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Toni Akeni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, inda ya yi zargin cewa ’yan Najeriya ba su gamsu da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

Ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyun adawa na samun taron jama’a masu yawa a wajen gangamin yaƙin neman zaɓensu.

Akeni ya zargi gwamnatin APC da ƙara tsananta talauci, tara basussukan ƙasashen waje da kuma kasa magance matsalar tsaro.

Ya kuma yi ikirarin cewa kusan ’yan Najeriya miliyan 3.7 ne ke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira 3,900 sakamakon rikice-rikice da hare-hare.

Ƙungiyar ta buƙaci ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, Donald Duke, Seyi Makinde, Peter Agada da Omoyele Sowore, da su ajiye burinsu na kashin kansu tare da haɗa kai wajen zaɓen ɗan takara guda.

A cewar Akeni, haɗin kan adawa zai ba su damar gabatar da ɗan takarar da zai mayar da hankali kan magance matsalolin ƙasar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *