Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke takarar Tukur Ribadu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ADC na gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2027, tare da umartar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta mayar da sunan Omar Suleiman a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Mai Shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa Suleiman ne ya samu mafi yawan ƙuri’u masu inganci a zaɓen fidda gwani na ADC, amma jam’iyyar ta sauya shi da Ribadu ba bisa ƙa’ida ba.

Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce Suleiman, wanda ɗan uwan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ne, ya shigar da ƙara ne domin ƙalubalantar matakin sauya shi da jam’iyyar ta yi.

A hukuncin da ya yanke ranar Juma’a, Mai Shari’a Egwuatu ya ce doka ba ta ba jam’iyya damar sauya ɗan takarar da ya lashe zaɓen fidda gwani ba, sai idan ya janye daga takarar da kansa ko kuma ya rasu.

Alƙalin ya bayyana cewa tun da Suleiman bai janye daga takarar ba kuma yana raye, matakin sauya shi da aka ɗauka ya saɓa wa doka, don haka ba shi da inganci.

Kotun ta umarci INEC da ta gaggauta mayar da sunan Omar Suleiman a matsayin halastaccen ɗan takarar ADC na gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *