Rahotanni da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta sun ce motar na ɗauke da kusan sojoji 60 ne a lokacin da haɗarin ya afku da misalin ƙarfe 10:30 na safiya, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin samar da kayan aiki.
- Majalisar Dokokin Cross River ta yi barazanar hana wasu ma’aikatu kasafin kuɗin 2027
- Sojojin Chadi sun shiga aikin tsaftace titunan N’Djamena
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata a haɗarin ba, haka kuma ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.
Motar ta kasance ta rundunar 27 Task Force Brigade da ke Buni Gari, jihar Yobe, amma har yanzu ba a samu sanarwar hukuma daga rundunar sojin Najeriya kan lamarin ba.
Ana jiran ƙarin bayani daga hukumomin soji domin tabbatar da halin da sojojin da abin ya shafa suke ciki da kuma cikakken bayani kan haɗarin.