Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya ce gwamnatinsa ta kashe sama da naira biliyan 35 wajen biyan basussukan fansho da alawus-alawus na ritaya da ta gada daga gwamnatin da ta gabata.
Obi ya bayyana cewa, baya ga biyan waɗannan basussuka, gwamnatinsa ta ƙaddamar da tallafin kuɗi na kowane wata ga tsofaffi masu ƙaramin ƙarfi waɗanda shekarunsu suka kai 75 ko fiye, ba su karɓar fansho kuma ba su da iyalan da za su iya kula da su.
- Jami’an Kwastam uku sun samu muƙaman fasaha da shaidar ƙwarewa a Hukumar Kwastam ta Duniya
- Sufeto Janar na ’yan sanda ya ƙaddamar da sabon ɗakin karatu a Kwalejin ’Yan Sanda ta Wudil
Ya ce shirin ya shafi kusan mutum 30,000, kuma an samar masa da tushen doka ta hanyar Dokar Tallafa wa Masu Ƙaramin Ƙarfi ta Jihar Anambra ta 2013, domin tabbatar da ci gaba da kula da irin waɗannan mutane.
A yayin da yake magana kan halin talauci da matsalar ƙarancin abinci a Najeriya, Obi ya ce ƙasar na buƙatar cikakken tsari da zai haɗa tallafa wa noma, bunƙasa ƙananan sana’o’i, samar da ayyukan yi da kuma kula da masu rauni, yana mai cewa ya kamata Najeriya ta koyi darussa daga ƙasashe irin su China da Indiya wajen rage talauci.