Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka tsakanin 2006 zuwa 2014 wajen rage talauci da inganta rayuwar mata, matasa, manoma da sauran masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Obi ya ce gwamnatinsa ta yi amfani da taswirar talauci domin gano ƙananan hukumomi da al’ummomin da suka fi fama da matsalar, ciki har da Anambra West, Orumba South, Awka North da Ogbaru, sannan ta mayar da hankali wajen samar musu da hanyoyi, tallafin noma da sauran abubuwan more rayuwa.

Ya bayyana cewa an tallafa wa dubban mata, zawarawa da masu ƙaramin ƙarfi da kuɗi da kayan sana’o’i, tare da samar da tsarin lamunin juyawa da tallafin ƙungiyoyin haɗin gwiwa domin ƙarfafa ƙananan sana’o’i da dogaro da kai.

Haka kuma, ya ce gwamnatinsa ta tallafa wa manoma ta hanyar shirin FADAMA, ta ba matasa 500 tallafin naira dubu 100 kowannensu bayan koyon sana’a, tare da raba kekunan guragu sama da 500 ga masu buƙata ta musamman.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *