Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya ƙaddamar da sabon ɗakin karatu mai ɗauke da sunansa a Kwalejin ’Yan Sanda ta Najeriya da ke Wudil, Jihar Kano, domin inganta harkokin karatu da bincike a rundunar.

Sabon ɗakin karatun yana da kujerun zama guda 1,000, tsarin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin kilowatt 30, ɗakin kallon shirye-shiryen bidiyo da labarai, da sauran sassan karatu na zamani.

An gina ɗakin karatun ne domin bai wa ɗaliban da ke karatun digiri na farko da na gaba damar samun ingantaccen yanayin karatu da bincike.

Bayan ƙaddamar da sabon ginin, za a mayar da tsohon ɗakin karatun kwalejin cibiyar karatu ta intanet, wato e-library, domin gudanar da bincike ta hanyar fasahar zamani.

Rundunar ’yan sandan ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na samar wa ɗaliban kwalejin kayan karatu na zamani, domin su samu ilimi da ƙwarewar da za su ba su damar yin gogayya da takwarorinsu a manyan jami’o’in Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *