Hukumar ta ce ta kama mai shekaru 35 a ranar 17 ga Nuwamba, 2026, a yankin Jere, yayin da aka cafke wanda ake zargin shi ne zai karɓi kayan, mai shekaru 30, a Gusau.
Haka kuma, an kama wasu mutane biyu da allunan magunguna masu haɗari, tare da ƙwato dubban ƙwayoyin Tramadol, Diazepam da Exol-5.
- Gambiya ta cafke mutane 94 da ake zargin shirin yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba
- An zargi masu shirya taron APC a Ibadan da kin biyan kuɗin mutanen da suka tara
A wasu samamen kuma, NDLEA ta ƙwato sama da tan 4.6 na tabar wiwi a Jihar Osun, da kuma tan ɗaya a Ondo, inda aka kama mutane da dama.
Ta kuma kama wasu da tabar wiwi, hodar ibilis, methamphetamine da makamai a jihohin Ogun, Edo, Katsina, Abia da Rivers.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, tare da buƙatar su ci gaba da ƙoƙarin dakile safarar miyagun ƙwayoyi da wayar da kan jama’a kan illolinsu.