Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna mutanen sun kewaye wata mota da ake zargin ta masu shirya taron ce, suna neman a biya su kuɗin da suka rage, tare da hana motar tafiya.
Mutanen sun yi zargin an yi musu alƙawarin Naira 5,000 kowannensu domin halartar taron, amma aka ba su Naira 2,000 kacal, inda suka ce ana bin su sauran Naira 3,000.
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada ƙudirin inganta kiwon lafiya
- ’Yan sanda sun kama ’yan uwa biyu bisa zargin kashe kawunsu a Bauchi
A cikin bidiyon, an ji wasu suna cewa ba za su bari motar ta wuce ba har sai an biya su kuɗinsu, yayin da waɗanda ake zargin masu raba kuɗin ne suka yi ƙoƙarin lallashin su, suna cewa kuɗin da suke da su ya ƙare.
Ba a tabbatar da waɗanda suka ɗauko mutanen ko kuma suka amince da biyan kuɗin ba, haka kuma babu wata sanarwa daga shugabancin APC a Oyo kan lamarin, ko bayanin ko an warware takaddamar.