Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum biyu bisa zargin kashe kawunsu mai shekaru 70, Alhaji Sa’idu Malam, a ƙauyen Jejin-Giwa da ke Burra, Ƙaramar Hukumar Ningi, bisa zargin maita.

Rundunar ta ce an gano gawar marigayin a gefen wani kogi a ranar 19 ga Nuwamba, 2026, da alamun raunuka a wuya, hannu da sauran sassan jikinsa, tare da kekensa, inda nan take aka kai gawar asibitin Burra, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Waɗanda aka kama su ne wasu matasa, masu shekaru 30, da shekaru 22, waɗanda binciken farko ya nuna cewa ’yan uwan marigayin ne, kuma ƙananan ’yan’uwan mahaifinsu.

’Yan sandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin, inda suka yi ikirarin kashe marigayin saboda zargin yana yi wa matansu sihiri, wanda suke ganin hakan ne ke jawo zubar da cikin matansu.

An kuma gano adda mai jini da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya jajantawa iyalan marigayin, tare da gargaɗin jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu bisa zargi ko camfi, yana mai cewa za a miƙa waɗanda ake zargin sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *