Samamen mai suna Operation Safe Horizon ya gudana ne ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026, a yankunan Tanji, Brufut, Batokunku da Kendingsebel, da ke yankin West Coast na Gambiya.
- Tinubu ya ce gyare-gyaren tattalin arziki za su rage kuɗin sufuri da na abinci
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada ƙudirin inganta kiwon lafiya
Cikin waɗanda aka cafke akwai ’yan Gambiya 49, ’yan Senegal 37, ’yan Guinea huɗu da ’yan Mali huɗu.
Haka kuma, akwai maza 80 da mata 13, ciki har da ƙaramar yarinya guda.
Hukumar ta ce ana tsare da mutanen a cibiyar kula da masu ƙaura da ke Tanji, inda ake gudanar da binciken su da sauran matakan da suka dace, yayin da ta jaddada ƙudirin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen yaƙi da ƙaura ba bisa ƙa’ida ba da safarar mutane.