Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ƙwararren ɗan wasan golf ɗan Afirka ta Kudu mai shekaru 37 da wata mai girki ’yar Kenya mai shekaru 25 bisa zargin safarar kilogiram 50.4 na tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira Loud zuwa Najeriya.

Hukumar ta ce an kama ɗan wasan, ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas ranar 11 ga Oktoba, 2026, bayan gano fakiti 46 na tabar wiwi a cikin akwatunansa.

Bincike ya nuna cewa shi da abokiyar tafiyarsa,, sun yi musayar akwatuna domin ɓoye ainihin masu kayan.

NDLEA ta ce an kama matar ne a ranar 15 ga Oktoba, lokacin da take ƙoƙarin barin Najeriya zuwa Kenya.

Ta bayyana cewa an yi mata alƙawarin dala 8,000 idan ta kai kayan inda aka nufa, yayin da aka yi wa ɗan wasan alƙawarin rand 5,000 na Afirka ta Kudu.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya ce ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na amfani da ’yan wasa da sauran ƙwararru wajen safarar kayayyakin haram, yana mai gargaɗin cewa babu sana’a ko matsayin mutum da zai kare shi daga binciken jami’an tsaro.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *