Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su ƙara ƙaimi wajen kare al’ummomin da ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga a Jihar Neja, bayan wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai.

Ƙungiyar ta ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 5 na safiyar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026, a ƙauyen Lumma Ba’are da ke Ƙaramar Hukumar Borgu, inda suka ƙona gidaje da shaguna tare da sace wasu mutane.

A cewar Amnesty International, maharan sun kai hari kan masallacin da mutane ke gudanar da sallar asuba, inda suka kashe dagacin ƙauyen da wasu masu ibada.

Ta kuma ce harin ya jefa al’ummar cikin firgici, yayin da har yanzu ba a san inda wasu mutanen da suka ɓace suke ba.

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda hare-haren ke ƙaruwa a yankin Borgu, inda yawancin mazauna ke dogaro da noma wajen samun abin rayuwa, amma yanzu suke tsoron zuwa gonakinsu.

Ta buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kawo ƙarshen hare-haren da ke addabar yankunan karkara.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *