Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Jungudo Haruna Mohammed, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, inda ya ce PDP ba ta shiga wata yarjejeniya da haɗakar ba, kuma ba ta ba kowa izinin wakiltar ta a taron ko amincewa da duk wani mataki da za a ɗauka da sunanta ba.
Jam’iyyar ta ce haɗakar da ta amince da ita a halin yanzu ita ce Rainbow Coalition, wadda take samun goyon bayan jagoranta na ƙasa, Nyesom Wike.
- Gwamnatin Jihar Kano za ta yi wa yara miliyan biyu rigakafi
- Kamfanin Dangote Coal ya tallafa wa ɗalibai 42 da tallafin karatu a Kogi
Ta kuma bayyana waɗanda ake gabatarwa a matsayin wakilanta a haɗakar a matsayin mambobin da aka kora daga jam’iyyar, waɗanda ba su da ikon yin magana ko ɗaukar mataki a madadinta.
PDP ta ce waɗannan mutane sun sha faduwa a shari’o’in da suka shigar a Kotun Tarayya, Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli, tare da zargin cewa kotuna sun hana Kabiru Tanimu Turaki, SAN, da abokan tafiyarsa bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar, sannan sun sanya musu tarar da ta haura naira miliyan 100 kan zargin amfani da kotuna wajen shigar da ƙarar da ba ta da tushe.