Kwamitin ya buƙaci shugabannin jami’o’in su riƙa bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, da kuma dokar Hukumar Kula da Daidaiton Wakilcin Ƙasa, domin tabbatar da adalci da daidaito wajen ɗaukar ma’aikata.
Ya ce sashe na 14(3) da 14(4) na kundin tsarin mulkin sun tanadi wakilcin jihohi da ƙabilu daban-daban cikin adalci a hukumomin gwamnati.
- PDP ta ƙaryata shiga haɗakar ƙungiyoyin adawa, ta ce ba za ta halarci taron 30 ga Nuwamba ba
- ADC ta zargi Tinubu da yin kunnen uwar shegu ga wahalar ’yan Najeriya
Wannan matsaya ta biyo bayan zaman sa ido da kwamitin ke gudanarwa, inda wasu jami’o’in gwamnatin tarayya daga yankin Arewa ta Tsakiya suka gurfana domin bayyana yadda suke gudanar da harkokin gudanarwa da ɗaukar ma’aikata.
Kwamitin ya jaddada cewa jami’o’in dole ne su tabbatar da gaskiya, adalci da dama daidai ga kowa wajen ɗaukar ma’aikata, maimakon barin bambancin yanki ko wasu muradu su rinjayi tsarin.