Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta haramta kashe kudi har Naira Biliyan 110 domin saya wa ‘yan Majalisar Dokoki ta Tarayya motocin alfarma da kuma biyan wasu kudaden alawus.
A cewar kotun, kashe kudin ya saba wa dokokin kundin tsarin mulki na kasa da kuma amana ga jama’a.
A hukuncin da ta yanke a ranar 6 ga Mayu, 2026, Mai Shari’a Yellim Bogoro, ta ce shirin kashe Naira biliyan 40 don sayen motoci 465 ga ‘Yan Majalisar Tarayya ya saba da dokokin sayen kadarorin gwamnatin tarayya.
Haka nan fitar da Naira Biliyan 70 domin biyan alawus ga sabbin ‘yan majalisa ya saba da tanade-tanaden dokoki da suka shafi na da’ar Ma’aikatan Gwamnati, da na rantsuwar kama aiki da ke kunshe cikin Kundin Tsarin Mulki Kasa.
Hukuncin ya biyo bayan wata kara da kungiyar kare hakkin dan Adam ta (SERAP) ta shigar, tana kalubalantar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a madadin zaurukan Majalisun biyu.
Mai Shari’a Bogoro ta kuma umarci Akpabio da Abbas da su tabbatar da cewa daga yanzu duk wata sayayyar da ta fitar da kudaden gwamnati da Majalisun ke bukatar yi, su yi la’akari da tanade-tanaden dokar kasa.
