Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya fice cikin fushi tare da katse wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na NBC ke yi da shi, biyo bayan takaddama mai zafi da ta barke tsakanin sa da mai gabatar da shirin.
Tattaunawar mai suna “Meet the Press,” wadda ‘yar Jarida Kristen Welker ke gabatarwa ta gudana ne a jihar Wisconsin, a ranar Lahadi 7 ga watan Yunin 2026 inda ta rikide zuwa cacar baki .
‘Yar Jarida Welker ta matsa wa shugaba Trump lambar ya kawo kwararan shaidu da za su gamsar da duniya kan ikirarin sa, cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa na shekarar 2020, da kuma zaben fidda gwani na jihar California da aka yi kwanan nan.
Sai dai Shugaba Trump ya tsaya a kan bakan sa cewa zaben Shugaban Kasa na shekarar 2020 kazamin zabe ne, ya kuma jaddada cewa har yanzu ana ci gaba da tafka irin wannan magudin a jihar California.
“Kwarai, an tafka magudi a zaben. Zabe ne mai cike da dauda. Kuma hakan na sake faruwa a yanzu haka a California… Suna tafka magudi a zaben,”- in ji Trump.
Lokacin da Welker ta matsa masa da ya kawo shaidar abubuwanda yake fada, shugaban ya bayyana cewa kiyasin sa ya ginu ne a kan abubuwan da idanunsa suka gani da kuma bayanan da yake samu daga mutane.
Tattaunawar ta sake daukar zafi lokacin da aka tabo dambarwar 6 ga watan Janairu na harin da masu zanga-zanga suka kai ginin Capitol Hill.
Welker ta tambayi Trump ko asusun dala biliyan 1.8 da yake son kafawa na musamman zai tallafa wa mutane 172 da suka amsa laifikan dukan Jami’an Tsaro.
Trump bai musanta hakan ba, inda ya yi ikirarin cewa jami’an hukumar bincike ta (FBI) ne da kansu suka tura mutane cikin ginin, kuma da yawa sun amsa aikata laifin ne kawai saboda tsoron daurin shekaru masu yawa.
Yayin da tattaunawar ta kai kololuwa, Trump ya ragargaji mai gabatar da shirin da wasu manyan kafafen yada labarai na Amurka kamar su ABC, CBS, CNN, da NBC da nuna son kai.
Daga karshe, Shugaba Trump ya kasa daurewa, inda ya daka wa mai gabatar da shirin tsawa da cewa “Ko dai ke Mayaudariya ce, ko kuma Wawiya.”
A karshe Shugaba Trump da kansa ya kawo karshen tattaunawar bisa hujjar gajiyawa da yayi da hirar.
Bayan fadin haka, Trump ya cire lasifikar da ke jikinsa, ya tashi tsaye, ya fice ya bar gurin tattaunawar, duk da cewa Kristen Welker ta tunatar da shi cewa ta yi tattaki ne daga Washington zuwa Wisconsin domin wannan hira.
Duk da cewa Trump ya dogara da wasu hujjoji game da magudin zaben Shugaban kasar a shekarar 2020, hukumar zaben Amurka da wasu hukunce-hukuncen kotuna daban-daban sun sha nuna cewar babu wata kwakkwarar shaida, da zata tabbatar da ikirarin sa.
Yan jarida a Amurka na zargin Trump da yawan fadar abubuwan da ba su da tushe ko hujja. Wannan ta sanya kafafen ke katse shi ko kalubalantar maganar sa yayin tattaunawa, matakin da Trump ke kallo a matsayin cin fuska, nuna son kai, da kuma yunkurin gano kurensa ko aibata shi da gangan.
