Wata mata tare da ’ya’yanta uku sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gundumar Maitama da ke Abuja
Matar da yaran nata sun sanya kayan makaranta tare da ɗaga kwalaye dake dauke da rubutu mai nuna halin rashin tabbas a makarantu, da nuna bukatar a ceto ɗaliban da aka sace a jahohin Borno da Oyo
- Kotu ta haramta saya wa ‘yan majalisa motocin Naira biliyan 110
- Gwamnati ta dubi halin da muke ciki a hannun Masu Garkuwa- Mai ‘Dakin Janar Rabe
- Remi Tunubu Ta tallafawa masu kananan Sanao’i a Abuja
Matar ta ce yanzu tana tsoron tura ’ya’yanta makaranta saboda yawaitar sace ɗalibai, sannan ta yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa wajen magance matsalar.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar 15 ga watan mayun daya gabata kungiyar Boko Haram ta sace dalibai 42 a karamar hukumar askira Uba a Jihar Borno, in da a lokaci guda aka sake sace wasu 39 a jahar Oyo.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na bayyana mamakin yadda mahukunta basu faye mayar da hankali kan karuwar rashin tsaro a sassan kasarnan, kamar yadda suke mayarwa kan harkokin siyasa ba.
