Tawagar Super Falcons ta Najeriya ta nuna bajinta, inda ta doke takwararta ta Senegal 3-0 a wasan zagaye na biyu da suka fafata a filin wasanni na Remo Stars, dake Ikenne, a ranar Litinin.

Ko a ranar Jumma’a, Kungiyar Falcons ta doke yan wasan Senegaldin da ci 2-1,a wasan su na farko,

Wasa ne na sada zumunci na kasa da kasa da kasashen biyu suka buga domin shirye-shiryen gasar cin kofin Afirka na Mata da za a yi a Maroko.

‘Yar wasan Najeriya, Joy Omewa, ta yi nasarar zura kwallaye biyu, sa’an nan kuma kyaftin din Super Falcons, Rasheedat Ajibade ta zura kwallo daya.

A Maroko, Falcons, da ke neman lashe kofin karo na 11, za su fafata da Masar, Zambia da Malawi da ke halartar gasar a karon farko a rukunin (C).

Yayin da Senegal za ta buga da mai masaukin baki Maroko, Algeria da Kenya a rukunin (A) na gasar da aka shirya daga 25 ga watan Yuli zuwa 16 ga Augusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *