Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Ojukwu, ta bayyana bacin ran ta, dangane da yadda hukumomin Afirka ta Kudu ke tafiyar da lamarin cin zarafi da tsoratar da ‘yan Najeriya a kasar.
Da take zantawa da manema labaran Fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin, Ministar ta yi watsi da ikirarin wasu hukumomin Afirka ta Kudu na cewa yawancin ‘yan Najeriyar da abin ya shafa baƙi ne da ba su da takardu.
Da aka tambaye ta ko wadanda ke neman dawowa gida galibi baƙi ne marasa takardu kamar yadda hukumomin Afirka ta Kudu ke ikirari, Ojukwu ta ce: “A ce ‘yan Najeriyar da ke Afirka ta Kudu suna gudanar da halastattun kasuwanci baƙi ne da ba su da takardu karya ne tsagwaron ta.”
Lokacin da aka tambaye ta ko Najeriya na iya daukar fansa ga ‘yan Afirka ta Kudu a Najeriya, Ambasadar ta ce, “wannan lamari ne da muke tattaunawa a matakin Gwamnati da Majalisun Tarayya.”
Ambassada Bianca Ojukwu ta ce, “Najeriya ba ta ji dadin abinda Afirka ta kudun ke yiwa ‘ya’yanta mazauna kasar ba, duk da sadaukarwa da Najeriya ta yi a baya wajen gwagwarmayar kwatar mata ‘yancin kai.
A ranar Litinin ne Gwamnatin Najeriya ta dage ranar da ta ayyana da fara kwashe ‘yan kasar ta 270 daga Afirka ta Kudu, daga baya aka dage aikin zuwa ranar Talata, sakamakon wasu dalilai.