Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Kwamitin Shugaban Kasa na Musamman kan Shirin Yaki da Cutar Ebola da sauran barazanar Lafiyar Jama’a da ke Kunno Kai. 

Kazalika, Tinubu ya ba da umarnin sakin Naira biliyan 10 nan take a matsayin kudin gudnar da aikin na gaggawa.

A cewar wata sanarwa daga mai baiwa Shugaban shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya wallafa, kudaden za su karfafa shirin gudanar da ayyuka na Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC).

Sanarwar tace shirin zai kuma tallafa wa muhimman ayyukan bayar da agajin gaggawa na lafiyar jama’a a kasa, domin kiyaye su daga barazanar kwararowar cutuka masu saurin yaduwa.

Kwamitin Shugaban Kasa na Musamman kan Ebola zai kasance karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, tare da mambobi daga ma’aikatu, hukumomi, masu ruwa da tsaki da kuma wakilan jihohi.

Cutar Ebola ta sake bayyana kwanan nan a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo (DRC) da Uganda, dukkansu makwabtan juna, lamarin da ya sanya Kenya rufe kan iyakokin ta.

Amincewar Shugaban ta biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka kira karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa don duba shirin Najeriya da kuma samar da dabarun dakile shigowar cutar cikin kasa.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci jihohin da ke da filayen jirgin sama, da na kan iyakokin kasa da kasa, Ma’aikatu da masu ruwa da tsaki su gabatar da tsare-tsarensu ga hukumar domin shiga tsakani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *