Matasan da ke sha’awar shiga aikin jandarma a Nijar sun yi gudun tsere a wani bangare na tankade da rairayar wadanda suka cancanci rubuta jarabawar da za a yi a nan gaba.
Kamfanin dillancin labarai na ANP ya wallafa hotunan yadda abubuwan suka wakana a jihohin Agadez Dosso Maradi da Tilabery
