Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya ba wa masu ruwa da tsaki a jihar Ekiti tabbacin cewa Hukumar ta kammala duk wani shiri na gudanar ingantacce kuma karɓaɓɓen zaɓen Gwamna, a ranar Asabar, 20 ga watan Yuni, 2026.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, yayin babban taron masu ruwa da tsaki kan zaben gwamnan jihar Ekiti da zai gudana a Birnin Ado-Ekiti.
Yayin da yake jawabi ga jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, kungiyoyin fararen hula, kafafen yada labarai, da sauran wakilai, Farfesa Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta riga ta tsara dabarun da za su tabbatar da nasarar zaben.
Shugaban ya bayyana cewa jimilar mutane Miliyan Guda da Dubu 59, da 360 da suka yi rajista ne za su sami damar jefa kuri’a a fadin kananan hukumomi 16 na jihar, mai Mazaɓu 117, da kuma Rumfunan zaɓe Dubu 2 da 445.
A cewarsa, wannan adadi ya hada da sabbin masu rajista Dubu 66, da 664, yayin da aka goge sunayen mutum Dubu 2 da 103, da basu inganta a zahiri ba.
Farfesa Amupitan ya kara da cewa shirye-shirye ta ɓangaren kayan zaɓe sun kammala, inda aka tsara buɗe rumfunan zaɓe da karfe 8:30 na safe a ranar zaben.
Ya kuma tabbatar da cewa an riga an horar da ma’aikatan wucin gadi, kuma ana aiwatar da tsarin rarraba kayan zabe kamar yadda jadawalin hukumar ya tanada.
Shugaban na INEC ya jaddada cewa za a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ta (BVAS), sannan za a dora sakamakon kowace mazaba kai tsaye a shafin duba sakamakon zabe na hukumar, wato (IReV), domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Haka zalika, INEC ta tanadi hanyoyin taimaka wa masu bukata ta musamman, ciki har da takardun zabe na musamman ga makafi da gilashin kara girman rubutu domin taimaka wa masu lalurar ido da zabiya.
Game da batun tsaro kuwa, Shugaban ya bayyana cewa hukumar tana aiki kafada da kafada da Kwamitin Hadin Gwiwa na Hukumomin Tsaro domin tabbatar da doka.
Haka kuma, hukumar tana hadin gwiwa da hukumomin yaki da rashawa na EFCC da ICPC, domin kakkabe duk wani yunkuri na sayen kuri’u ko wasu laifukan almundahana a ranar zabe.
Prof. Amupitan ya kuma sanar da cewa hukumar ta amince da kafafen yada labarai guda 91 dauke da ‘yan jarida 675 domin yada labaran zaben, tare da kungiyoyin sa ido guda 98, (96 na gida, da kuma 2 na kasashen duniya).
Baya ga zaben gwamnan jihar Ekiti, Shugaban na INEC ya sanar da cewa hukumar za ta gudanar da zabukan cike gurbi na ‘yan majalisa guda shida a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers, Ondo, Kano, da Kebbi, a daidai wannan rana.