Ya zuwa yanzu, Afirka ta Kudu ta gane matsayin ta a idon kasashen dake Nahiyar

A duk lokacin da gangar wasannin motsa jiki ta kankama, al’adar mutanen Nahiyar Afirka ita ce dunƙulewa waje guda, domin marawa duk wata ƙasa da ta samu fitowa daga cikin ta baya.

Manazarta na kallon hakan a matsayin jini ɗaya da ya ratsa jijiya, dake haifar da son juna da haɗin kan baƙar fata.

Sai dai, a wannan karon, tarihin ya sauya salo, wanda hatta dandalin sada zumunta bai  bari an bar shi a baya ba, ganin yadda shafukan suka barke da wani sabon saƙo na daban.

Wasan bude gasar cin kofin duniya ta 2026 da aka fafata tsakanin ƙasar Afirka ta Kudu da Mexico ya fito da wani ɗaci dake binne a zukatan miliyoyin ’yan Afirka.

Fushin da aka daɗe ana tsimawa game da matsalar kyamar baƙi da korar ’yan uwa da ake yi a ƙasar, zai bar da ƙura.

Maimakon a ji hargowar murna da addu’o’in nasara ga kungiyar Bafana Bafana, yaƙin cacar baka a Dandalin intanet a sassan Afirka, ya cika ne da fatan nasara ga ƙasar Mexico, dake yankin Turai.

Wannan lamari ya wuce batun wasan ƙwallon ƙafa kawai, ya zama babban raddi na siyasa da zamantakewa.

Bikin bude gasar cin kofin ta bana a Mexico

Kafafen Sada Zumunta Sun Dauki Dumi: “Babu Goyon Baya Ga Masu Korar Baƙi”

Tun kafin a busa tashi, shafukan X (da aka sani da Twitter) da Facebook da Instagram sun cika makil da raddi mai zafi daga sassan Afirka daban-daban, musamman daga ƙasashe irin su Najeriya, Ghana, Zimbabwe, da Kenya.

Ga kadan daga cikin misalai

“Ta yaya za mu taya ku murnar cin ƙwallo, bayan kuna farautar ’yan uwanmu baƙar fata a kan titunanku? Yau kowa da rigar Mexico yake kallo!”— Wani matashi daga Legas, Najeriya.

Wani kuma daga ƙasar Zimbabwe, wadda ita ce maƙwabciyar Afirka ta Kudu ta kusa, cewa yake-

“Kwallon ƙafa wasa ne na zaman lafiya da ƙaunar juna. Idan ba kwa son mu a raye cikin ƙasar ku, kada ku nemi soyayyar mu a filin wasa. Mexico ana tare!”

Sai dai tsohon dan wasan Najeriya Sunday Oliseh, na ganin matsin lamba ce ta yiwa ‘yan wasan yawa, shi yasa aka mamaye su-

“Abin da ya faru da Afirka ta Kudu ba laifin mai horaswa ba ne, kuma ba wai Mexico ta fita iya bugawa ba ne. Matsin Lamba ce ta yi musu yawa. Idan kana buga wasan bude gasa a gida, kuma daukacin duniya da dandalin sada zumunta na kallon ka, idan ba ka da kwarewar daurewa, gwiwarka sanyi za ta yi.” -Inji Oliseh

Tsohon dan wasan Najeriya Sunday Oliseh

Wadannan kalamai sun nuna cewa mutane da yawa sun yi amfani da wannan wasa a matsayin bulala ko makami na nuna bacin ransu ga take-taken gwamnati da al’ummar Afirka ta Kudu.

Yadda Kasashen Afirka Suka Guji “Bafana Bafana”

Abin da ya fi ba da mamaki a wannan dambarwa shi ne yadda ko da maƙwabtan Afirka ta Kudu na jini—ƙasashe irin su Zimbabwe, Mozambique, da Lesotho—ba su ɓoye goyon bayansu ga ƙasar Mexico ba.

Wannan ya faru ne saboda yawancin mutanen da ke mutuwa ko rasa dukiyoyinsu yayin hare-haren kyamar baƙi a Afirka ta Kudu, ’yan waɗannan ƙasashe ne da ke tsallakawa da nufin neman abinci.

A cikin biranen makwaftan kasashen, an rinka samun rahotannin cewa a duk lokacin da Mexico ta kai hari kusa da ragar Afirka ta Kudu, shagunan kallon ƙwallo na cika da ihu da tafi na farin ciki.

Wannan hantara ta fito fili, inda aka rinka yi wa ’yan Afirka ta Kudu da ke zaune a wasu ƙasashen ba’a, ana gaya musu cewa ƙasarsu ba za ta je ko’ina ba muddin ba su canza halinsu ba.

Yan wasan Bafana Bafana

Darasi daga Filin Wasa

Wannan dambarwa ta nuna cewa duniyar yau ta sauya, domin ba za ka iya shuka ƙiyayya da daddare, sannan ka sa ran girbar soyayya da rana ba.

Yayin da Afirka ta Kudu ta yi ta yayata cewa gasar “ta ‘yan Afirka ce zalla,” sauran ’yan nahiyar sun nuna musu cewa haɗin kai yana farawa ne daga yadda kuke cin abinci da maƙwabcinka a gida.

A Karshe! Wasan ya ƙare, amma saƙon da ’yan Afirka suka aika wa Afirka ta Kudu ya nuna a aikace- “Idan kuna son goyon bayan Nahiyar, dole ne ku mutunta jinin ’yan nahiyar”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *