Babbar Kotun Jihar Filato ta yanke hukunci cewa duk wani Bahaushe da aka haifa kuma aka yi renonsa a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, ya zama ɗan asalin yankin.
Mai shari’a C. Donglong ce ya bayar da hukuncin yayin da yake yanke hukunci a wata kara da aka shigar, domin ƙalubalantar wariyar da ake nunawa yaran da aka haifa a Jos ta Arewa.
Masu ƙara Fatima Baba Akawu, da Baba Alhaji Akawu, sun maka ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa gaban kotun, sakamakon hana mai kara ta farko takardar shaidar zama ƴar asalin gari.
Mai ƙara Fatima Baba Akawu ta shaidawa kotun cewar an haifa tare da rainonta a Jos ta Arewa, amma ƙaramar hukumar da aka haife ta hana ta takardar zaman ƴar asalin gari.
Madadin haka, karamar hukumar ta ba ta “Takardar Zama” kawai, ba tare da la’akari da illar hakan ga rayuwar ta ba.
Mai ƙarar yayi misali da yadda ƙaramar hukumar ke fifita sauran ɓangarori na ƙabilu akan saura, duk da cewa tare aka haife su har suka girma, hakan ba ya sanya wa ayi mata kallon ƴar asalin gari.
-
Majalisar Dattawa ta nesan ta kanta da umarnin kama Mele Kyari
-
Majalisar Wakilai ta amince da kafa ƴan Sandan Jihohi
Da yake yanke hukunci a ranar Talata 9 ga watan Yunin 2026, Mai shari’a Donglong ya amince da dukkan bukatun masu ƙara.
Alkalin ya umurci Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta baiwa Fatima Baba Akawu Takardar Shaidar zama ƴar Asalin Gari, kamar yadda ake baiwa kowa.
Mai Shari’ar yace, duk wani ɗan asalin gari, ba tare da la’akari da asalin kabilar sa ba, yana da cikakken hakkin samun Takardar Shaida daga yankin da yake.
Alkalin, yayin kafa hujja da Kundin Tsarin Mulki na 1999, ya ayyana cewa “Takardar Zama” ba ta da wani tushe a dokokin Najeriya, bata da asali kuma ba ta da wani tasiri na shari’a ko kadan.
Alkalin ya jaddada cewa fifita wani ƙabila akan wani kamar yadda aka yiwa mai ƙarar tamkar nuna wariya ne, wanda ya saba da Sashe na 42(1), 42(2), 15(2), 17(2)(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Sannan hakan tamkar yin zagon ƙasa ne ga Matakai na 2 dana 3 na yarjejeniyar ƙasashen Afirka game da ƴancin Ɗan Adam da Al’umma.