An kama mai safarar makaman ne bayan daukar lokaci ana bibiyar sa

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun dakile wani yunkurin kai makamai ga ‘yan bindiga bayan sun kama wani da ake zargi da safarar makamai masu haɗari zuwa ga wani shugaban ‘yan bindiga a Zamfara.

An kama wanda ake zargin ne a Ƙaramar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano bayan samun bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu akan sa.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin na kan hanyarsa daga Maigatari ta Jihar Jigawa zuwa Funtua a Jihar Katsina domin isar da tarin makamai ga masu aikata miyagun laifuffuka.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigogin AK-47 guda uku, rokoki guda huɗu tare da harsasai  da kuma kwanson alburusai.

Binciken farko ya nuna cewa makaman na da alaƙa da wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da ke addabar wasu yankunan Jihar Zamfara.

Wanda ake zargin ya amsa cewa an ɗauke shi aiki ne domin kai makaman, inda aka yi masa alƙawarin Naira dubu 450 bayan ya kammala aikin.

Hukumar DSS ta ce tana ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a wannan haramtacciyar sana’a da kuma lalubo hanyar da ake bi wajen kai makamai ga ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *