Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar bakin ciki game da rasuwar  Manjo-Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu yayin da yake hannun ‘yan ta’adda a Jihar Katsina.

Cikin wata sanarwa da mataimakawa masa a ɓagaren yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, Shugaban ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, musamman matarsa wacce har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane, tare da jajantawa Gwamnatin Jihar Katsina da rundunar sojin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta taba amincewa da bukatun ‘yan ta’adda kafin sakin wadanda ake tsare da su ba, yana mai cewa dole ne su mika wuya ko su fuskanci cikakken karfin doka.

Ya kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da yaki da ta’addanci har sai an kawar da shi gaba daya, yana mai kira ga hadin kan ‘yan kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa Janar Abubakar, na kan hanyarsa ta zuwa garinsu ne lokacin da ‘yan bindiga suka yi masa kwanton bauna suka sace shishi

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *