Waɗansu da ake kyautata zaton Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun banka wa makarantar firaimare da Sakandire wuta a kauyen Kautikari da ke Karamar Hukumar Chibok a Jihar Borno.

Wannan na zuwa ne bayan kwashe kimanin wata Daya da sace yara dalibai ƴan firaimire da Sakandire da ke Askira-Uba, wanda kawo yanzu babu labarin su.

Jami’an tsaro sun ce an afka wa garin wanda yasha fama da hare-haren Ƴan Boko Haram da misalin karfe 7 na maraicen Asabar.

“Babu rasa rai sai dai al’ummar garin sun bazama cikin daji don tsira da ransu,” inji wani makocin garin.

Wani magidanci da ya buka ci a sakaya sunan sa, yace ‘yan ta’addar sun shiga kauyen watannin baya amma basu barnatar da kayan Jama’a ko na Gwamnati ba.

“Nayi mamaki ta yadda suka banka ma makarantun Gwamnati guda biyu wuta. Harin yasha banban da saura.

Anyi kokarin magana da mai magana da yawun hukumar Yan sanda, ASO Nahum Kenneth Daso, amma haƙa bata cimma ruwa ba.

Yankin na Chibok yana fama da hare-haren mayaƙan, wanda anan ne aka fara kwashe ɗalibai Mata na Sakandire shekaru da dama da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *