Wata Tawagar Hedikwatar tsaro ta kasa ta isa birnin Katsina domin ta’aziyya ga gwamnatin jihar bisa rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar Mai ritaya.

Shugaban tawagar Manjo Janar IM Abdullahi ya bada tabbacin hedkwatar ta lashi takobin zakulo wadanda ke da alhakin kisan.

Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal, ya ce gwamnatin su zata bayar da dukkanin goyon bayan da Hedikwatar tsaron ke buƙata, domin cimma wannan nasara.

Mal Faruk Lawal ya bayyana cewa gwamnatin Jihar na iyakacin  kokarin ta, sai dai ta na buƙatar tallafi daga hukumomin tsaro domin fatattakar bata gari.

A ranar Asabar 13 ga watan Yuni ne Gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar Manjo Rabe a hannun ƴan bindiga, bayan gaza cimma matsayar sako musu ƴan uwa da aka kama a matsayin musaya.

Al’ummar ƙananan hukumomin jihar Katsina sun shafe tsawon lokaci ƙarƙashin matsin ƴan bindiga dake sace su domin karɓar kuɗin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *