Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti, Dakta Wole Oluyede, ya yi zargin cewa ana tsoratar da masu kada kuri’a a wasu rumfunan zabe yayin gudanar da zaben gwamna na yau Asabar.

Dakta Oluyede ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a Osaguru, Runfa ta 6 a Gunduma ta 3 da ke Ikere-Ekiti. Ya kuma nuna rashin jin dadinsa game  da yadda ake kada kuri’a cikin jinkiri a rumfar zabensa.

 

 

Ya bukaci hukumomin da ke kula da zaben su tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci ba tare da tsoratar da masu kada kuri’a ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *