Masu zaɓe sun nuna damuwa kan tsarin jerin layi, inda suke bukatar da a ba ma tsofaffi da mata masu juna biyu fifiko.

A mazaba ta 9 rumfa na 6 dake unguwar Adebayo, a Jihar Ekiti, mutane da dama sun riga sun kaɗa ƙuri’arsu cikin kwanciyar hankali, kamar yadda masu sa ido suka tabbatar.

Bangaren mazabar Ikere Ekiti, an samu rahoton cewa wani mai kaɗa ƙuri’a ya suma a layi, amma an ba shi taimako yayin da zaɓen ya ci gaba.

An samu ɗan tashin hankali bayan wani ɗan majalisa ya nuna ƙuri’arsa, a mazabar Ikere, amma jami’an tsaro sun daidaita lamarin.

Rahotanni da muka samu a mazabar yammacin Jihar Ekiti, an fara tantance masu zaɓe, sai dai an lura da rashin baturen zaɓe a wurin, yayin da mataimaka ke kula da aikin.

A Ido/Osi , an hango jami’an tsaro biyu, yayin da wasu wakilan jam’iyyu ke rabawa masu zaɓe ababen motsa baki. An kuma lura da wasu mata da ke rubuta sunayen mutane da kuma ba wasu lambobi, lamarin da ake ci gaba da tantancewa.

Gaba ɗaya, rahotanni sun nuna cewa zaɓen na gudana cikin kwanciyar hankali a yawancin wuraren da ake sa ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *