Kaɗa kuri’u ya Fara cikin lumana a yawancin wuraren

Rahotanni daga masu sa ido kan zaɓen gwamnan Jihar Ekiti sun nuna cewa an fara tantance masu zaɓe da kuma kaɗa ƙuri’a a yawancin rumfunan zaɓe da ke sassa daban-daban na jihar.

A Ilawe Ekiti, rumfa ta 5 dake cikin Adin Quarters, an fara kaɗa ƙuri’a da tantance masu zaɓe a rumfunan zaɓe shida, yayin da jami’an zaɓe suka kuma wayar da kan alumma akan sayen ƙuri’a.

A  bangaren Ado-Ekiti da Ikere Ekiti, an tabbatar da cewa an fara kaɗa ƙuri’a, inda masu zaɓe ke ci gaba da yin tururuwa a rumfunan zaɓe domin kada ƙuri’a.

Sai dai a Ado-Ekiti, an samu takaddama kan layi tsakanin masu zaɓe, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya.

Haka ma a yankin Emure, rahotanni sun nuna cewa ana gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali a rumfar zaɓe ta 015 da ke Ogbontioro.

A Gabashin Ekiti kuma, an samu wasu zarge-zarge kan ware wasu masu zaɓe bayan kaɗa ƙuri’a, sai dai har yanzu ana ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Gaba ɗaya, rahotanni sun nuna cewa zaɓen na gudana cikin kwanciyar hankali a yawancin wuraren dake cikin Jihar Ekiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *