A yau ne al’umar jihar Ekiti ke zaɓen sabon gwamna don mulkar jihar a shekaru huɗu masu zuwa. Rahotanni dake ishe mu na nuni da ce tuni masu kaɗa ƙuri’a suka fita rumfunan zaɓe.
An ga jami’an ‘yan sanda da na hukumar tsaro ta NSCDC, kuma an ruwaito cewa kayan zaɓe da turawan zaɓen sun isa rumfunan zaɓe daban-daban.
Yayin da a wasu rumfunan zaɓe an fara tantance masu zaɓe kan lokaci, a wasu wuraren, matsalar na’ura ta kawo wa fara tantancewar cikas.
- EKiti 2026: Meyasa Ekiti ke gudanar da zaben ta da ban da sauran Jihohi
-
Zaɓe a Ekiti: An fara kaɗa ƙuri’a duk da kananan takaddama a wasu wuraren
-
Zaɓen Gwamnan Ekiti: Tarihin siyasa da yanayin hamayya a jihar
Ya zuwa yanzu an samu rahotannin fara kaɗa ƙuri’u a wasu sassan jihar.
Rahotanni daga masu sa ido kan yadda ake gudanar da zaɓen gwana a jihar Ekiti sun nuna cewa tun misali karfe 8:44 aka fara kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 013, a unguwar Public Park dake ƙaramar Hukumar Ikere.
Har ila yau, rahotoanni da hukumar CJID MiNE dake sa ido da kuma bibiyar zaɓen jihar Ekiti a yanzu haka, sun nuna an fara kaɗa ƙuri’a, a cibiyar zaɓen dake Christ Primary School ta ƙaramar hukumar Ijero, rumfar zaɓe mai lamba 001, inda aka bai wa masu manyan shekaru damar fara jefa nasu ƙuri’un. Sai dai, ba a tanadar musu kujerun da za su zauna ba.