• Mazauna Zamfara Sun Yi Murna Bayan Sojoji Sun Yi Nasara Kan ‘Yan Bindiga a Gummi

Mazauna wasu yankuna na Jihar Zamfara sun nuna farin ciki bayan da dakarun sojin Najeriya suka samu gagarumar nasara kan ‘yan bindiga a safiyar Asabar a ƙaramar hukumar Gummi.

A cewar bayanan da aka samu, samamen ya shafi ƙauyukan Falale da Tungan Waka da Birnin Magaji da Kwakwani da Dan Gulbi da kuma Naniya.

Rahotanni sun ce an kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar, yayin da aka kama wasu da ransu. Haka kuma, dakarun sun kwato babura masu yawa da kuma dabbobin da aka yi garkuwa da su.

Bayan kammala farmakin, mazauna yankunan sun tarbi dakarun cikin murna, inda suka yabawa ƙoƙarin da suke yi na dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.

 

Abbas Ismail Dinki Gummi

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *