Yayin da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti ke gudana, an fara samun rahotannin zargin sayen ƙuri’u a sassan jihar.
Wani rahoton cibiyar bincike ta (Dataphyte), ya ce ana baiwa masu jefa ƙuri’a Naira Dubu 5 ko fiye da haka domin sayen kuri’unsu.
Rahoton na Dataphyte yace abune mai tayar da hankali ganin yadda wasu ‘yan siyasa ke sayen kuri’u, abinda ka iya sanya shakku game da sahihancin zaɓen, ko kuma dokar hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta ayyana hakan a matsayin laifi.
- Zaben EKiti: Dan Takarar Gwamna na jam’iyyar PDP Dakta Wole ya zargi ana tsoratar da masu kada kuri’a
- Ga ƙarin bayani kan yadda zaɓe ke gudana a Jihar Ekiti
A wani faifan bidiyo da Dataphyte ta wallafa a shafinta na X, anga wakilin wasu jam’iyyu a kananan hukumomin daban-daban na rubutawa tare da mika wa wadanda suke jefa ƙuri’a wasu takardu.
Wani faifan bidiyon ya kuma nuna yadda ake baiwa wasu da suka jefa ƙuri’a Naira Dubu Goma-Goma, bayan bayyana hujjar abinda suka zaba ga wasu mutane a gefe.
Rahoton yace al’amarin na siyen ƙuri’a ya faru a ƙananan Hukumomi da dama ciki har da Ilejemejena, inda ake sayen kuri’un masu zaben ta hanyar rarraba ƙananan takardu masu lambobi ga wadanda suka kada kuri’ar, Sai dai rahoton na Dataphyte bai tabbatar da ainihin manufar wannan mataki ba.
An kuma ruwaito irin wannan a yankin Eleyowo market/Odoba Gidado a Jihar ta Ekiti, inda masu sa ido suka ga yadda ake tura masu jefa ƙuri’a zuwa wani wuri na musamman domin ba su kuɗi.
A wasu rumfunan zaɓe kamar Odo Emure 1, Iye, da yankin Peter Adesina store, rahoton yace ana ba da kuɗi ga masu jefa ƙuri’a domin suyi zaɓe
An kuma ruwaito irin wadannan zarge-zargen rinjayar masu jefa ƙuri’a da tsoma baki a rumfunan zaɓe a sassa daban-daban na ƙananan hukumomin Ekiti East, Ido/Osi, Ijero, Ikere da Ado.
Mafi yawan rahotannin sun nuna cewa wakilan jam’iyyu na rubuta bayanan sirri na masu jefa ƙuri’a, ba su lambobi ko alamu, sannan kuma ana bin su bayan sun kammala zaɓe.
A ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta kasa dai, sayen ƙuri’a da kowanne irin kamfen a ranar zaɓe laifi ne da kan iya jawo tarar Naira Dubu Dari Biyar, ko kuma ɗaurin watanni Goma sha Biyu a kurkuku, ko kuma duka biyun.
