Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da sabon jirgin sama kirar (Boeing 747) da Qatar ta bashi kyauta, lokacin da ziyarci gaba s ta tsakiya a watan Mayun shekarar 2025.
Da yake kaddamar da jirgin a Ranar Asabar, Trump ya bayyana jirgin da cewa jirgi ne na alfarma, da aka kera shi a wani mataki da bai zama lallai a sake kera irinsa anan gaba ba.
Trump ya yi watsi da sukar da ake masa game da karbar kyautar, wadda daga bisani ya sadaukar da ita ga Ofishin Shugaban Kasar Amurka a matsayin jirgin (Air Force One).
- Hare-haren Rasha a Ukraine sun lalata wuraren Ibada
- Hotunan Ambaliya a Birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar
An ruwaito cewa kyautar ta zo ne a matsayin girmamawa daga Masarautar Qatar ga Shugaban Amurka, yayin wata ziyarar da ya yi wa kasashen yankin Gabs da tsakiya a shekarar data gabata.
Sai dai kuma lamarin ya haifar da muhawara a kafafen yada labarai da kuma masu sharhi kan siyasa da harkokin diflomasiya.