Zababben Gwamna Jihar Ekiti Abiodun Oyebanji ya gode wa al’ummar Jihar Ekiti bisa irin goyon baya da amincewar da suka nuna wa gwamnatinsa

Oyebanji na bayyana godiyar ne jim kadan bayan Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar a karo na biyu karkashin jam’iyyar APC

Ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shirye da ke nufin inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma, da kuma jin daɗin rayuwar al’umma gaba ɗaya

Gwamnan ya kuma yi kira ga abokan takararsa da sauran masu ruwa da tsaki da su ajiye bambancin siyasa, su hada kai domin ci gaban jihar Ekiti

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *