Zababben Gwamna Jihar Ekiti Abiodun Oyebanji ya gode wa al’ummar Jihar Ekiti bisa irin goyon baya da amincewar da suka nuna wa gwamnatinsa
Oyebanji na bayyana godiyar ne jim kadan bayan Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar a karo na biyu karkashin jam’iyyar APC
Ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shirye da ke nufin inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma, da kuma jin daɗin rayuwar al’umma gaba ɗaya
- Zaɓen EKiti 2026: APC ta yi nasara a Mazaɓar tsohon Gwamna Ayo Fayose
- Ƙananan Hukumomi 16 na Jihar Ekiti da zaɓen gwamna ya gudana cikin su
- Ana sayen kuri’u a zaben Ekiti- Rahoto
Gwamnan ya kuma yi kira ga abokan takararsa da sauran masu ruwa da tsaki da su ajiye bambancin siyasa, su hada kai domin ci gaban jihar Ekiti