Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdulaziz Abubakar ya ƙaryata rahotannin da ke danganta shi da ɗaukar nauyin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Tinubu.
Cikin wata sanarwa da Tsohon Shugaban Ma’aikatan sa Honarabul Abdullahi Abdulkarim Tsafe, ya sanya wa hannu a Gusau ranar Asabar, ya bayyana lamarin da ƙirƙirarre kuma abin dariya.
“Bari a bayyana a fili kuma ba tare da wata shakka ba cewa Sanata Abdulaziz Abubakar Yari ba shi da wata alaƙa ko kaɗan da duk wata zanga-zangar da aka shirya yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” in ji Tsafe.
Ya bayyana zargin a matsayin ƙarya da ɓatanci, mai dauke da manufar siyasa don ɓata sunan mutane.
A cikin makon da ya gabata aka dinga yaɗa jita-jitar shirya zanga-zangar adawa da salon gwamnatin Tinubu, wadda akace ta fito ne daga ofishin Sanata Abdul-aziz Yari.