Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Waidi Shaibu, ya umarci sabbin sojojin da suka kammala horo a rukuni na 90 a makarantar horas da kuratan sojoji dake Zaria, da su kasance masu ƙwazo da jajircewa wajen yaƙar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka, tare da kiyaye ƙwarewa, ladabi, da mutunta haƙƙin ɗan Adam.
Janar Shaibu ya bayar da wannan umarni ne a ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026, yayin bikin yaye sabbin sojojin da aka gudanar a Depot da ke Zaria, Jihar Kaduna kamar yadda kanfanin dillanci labarai na kasa NAN ya ruwaito
Ya bayyana cewa sabbin sojojin sun samu cikakken horo mai tsauri a fannonin yaƙi da ta’addanci da yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, domin su taimaka wajen ƙarfafa tsaron ƙasa da kare rayuka da dukiyoyin al’umma
- Yadda muke son Rundunar Sojan Najeriya ta koma-Waidi Sha’aibu
- Hedikwatar tsaron Najeriya ta lashi takobin zaƙulo waɗanda suka kashe Janar Rabe
- Hare-haren Boko Haram a yankunan Chibok na neman dawowa
Babban Hafsan Sojin ya kuma buƙace su da su bi ƙa’idojin aiki a fagen yaƙi, su kiyaye sirrin aikin soja, sannan su guji amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da za ta iya kawo matsala ko barazana ga tsaro.
Shuaibu ya sake jaddada aniyar Rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa baki ɗaya.
