Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da titin da ya taso daga Bill Clinton Drive zuwa Unguwar Tungar Madaki dake daf da hanyar sauka da tashin jiragen Sama  na Nnamdi Azikiwe dake Abuja

Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, yace sabuwar hanyar za ta buɗe muhimman hanyoyin bunƙasar tattalin arziki ga al’ummomin da suka shafe shekaru cikin keɓantacciyar rayuwa.

Akpabio yace hakan zai kuma rage musi raɗaɗin rashin adalcin da suka daɗe suna fuskanta daga gwamnatocin baya, bayan karɓe filayen da suka gada domin faɗaɗa filin jirgin sama.

A nasa jawabin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, yaba wa mutanen Tungan Madaki saboda haɗin kai da suke baiwa gwamnati wajen gudanar aikin

Acewarsa, maimakon neman makudan kuɗaɗen diyya, alummomin yankin sun nemi abubuwan more rayuwa da zai kawo musu cigaban da duniya ke tinƙaho dashi.

Wike ya kuma umurci kamfanin da ke aikin, CCECC, da ya kammala ƙarashen hanyar Tungan Madaki zuwa Zuba kafin ƙarshen Shekarar 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *