Zaɓen gwamnan Jihar Ekiti na shekarar 2026 ya gudana cikin lumana a mafi yawan sassan jihar, sai dai ƙarancin fitowar masu zaɓe ne ya fi ɗaukar hankali a rumfunan zaɓe da dama.

Rahotanni daga masu sa ido sun nuna cewa jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kasa INEC, kayan zaɓe da jami’an tsaro sun isa mafi yawan rumfunan zaɓe akan lokaci, lamarin da ya ba da damar fara yin zaɓe a wurare da dama.

A wasu ƙananan hukumomin Jihar, an gudanar da zaɓen cikin natsuwa ba tare da wata babbar matsala ba. Sai dai tun kafin tsakar rana, layukan masu kaɗa ƙuri’a sun fara raguwa a wurare da dama, yayin da wasu rumfunan suka kusan kammala zaɓe da wuri.

Duk da an samu matsalolin na’urar BVAS a wasu rumfunan, an samu bambanci tsakanin adadin waɗanda aka tantance da waɗanda suka kaɗa ƙuri’a, a wasu wuraren kuma kasa tantancewar akayi.

Haka kuma, masu sa ido sun ruwaito zarge-zargen sayen ƙuri’u da tasirin jami’an jam’iyya a wasu yankunan, sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a samu cikakkiyar tabbatarwa daga hukumomin da abin ya shafa ba.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an zaɓe (POs) na ci gaba da mika na’urorin BVAS da sauran takardu zuwa ga jami’an tattara sakamako (SPOs), yayin da ake haɗa sauran kayan aiki domin kai su ofishin INEC.

Haka kuma, jami’in tattara sakamako (SPO) tare da wasu jami’ai sun bar cibiyar zuwa ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa INEC.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an riga da an mika sakamakon rumfunan zaɓe 15, duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanan sauran ba.

An tattara wannan bayanin ne daga rahotannin masu sa ido na (CJID MiNE) da suka bibiyi yadda zaɓen ya gudana a rumfunan zaɓe daban-daban a faɗin Jihar Ekiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *