Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da kuɗaɗe daga Asusun ko ta kwana kan barazanar cutar Ebola da cutuka masu haɗari (OIRF).

Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Ali Pate ne, ya bada izinin fitar da kuɗaɗen, inda za’a baiwa kowacce jiha kaso 50 cikin 100, wanda ya kai Naira Miliyan 21.2.

Za a fitar da kuɗaɗen ne ƙarƙashin hukumar kula da ƙananan cutuka ta ƙasa, a shirin ta na baiwa al’umma kulawar data dace (BHCPF)

Kawo yanzu dai babu rahoton ɓullar cutar a Najeriya, gwamnati ta ce ta ɗaukar matakai ne, domin taimaka wa ƙoƙarin ko ta kwana.

Haka kuma tsarin zai kyautata shirin da  jihohin ke da shi na yaƙi da cututtuka masu saurin yaɗuwa,  kariya da kuma ɗaukar matakan gaggawa daga tushe.

Farfesa Pate ya kuma umarci jihohin da za su yi amfani da tallafin da su gabatar da cikakken bayanin yadda suka kashe kuɗaɗen da aka ba su a baya da kuma na yanzu cikin watanni shida

Cutar Ebola na cigaba da yaɗuwa cikin sauri a Jamhuriyar Kongo, lamarin da ya sanya maƙotan ƙasashe irin su Rwanda da Kenya rufe kan iyakokin su.

Matakin ya sanya sauran ƙasashen Afirka ciki har da Najeriya zama cikin shirin ko ta kwana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *