Mai Girma Abiodun Abayomi Oyebanji shi ne wanda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, wato INEC, ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka kamala a jihar Ekiti.

Zaɓaɓɓen Gwamnan na Jihar Ekiti Abiodun Abayomi Oyebanji dai an haife shi ne a ranar 21 ga Disamba, 1967, a garin Ikogosi-Ekiti. Ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti.

Ya fara karatunsa ne a Makarantar Firamare ta Baptist da ke Ikogosi-Ekiti. Daga nan ya halarci Awo Community High School, sannan ya koma C.A.C. Grammar School da ke Efon-Alaaye a Jihar Ekiti a shekarar 1979. Bayan haka ya yi karatu a Federal School of Arts and Science a Jihar Ondo da kuma District Commercial Secondary School da ke Aramoko-Ekiti tsakanin shekarun 1983 zuwa 1985.

A shekarar 1989, ya samu digirin farko na Kimiyyar Siyasa (B.Sc. Political Science) daga Jami’ar Jihar Ondo (wadda yanzu ake kira Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti). Daga baya, a shekarar 1992, ya samu digiri na biyu (M.Sc.) a fannin Kimiyyar Siyasa, musamman a harkokin hulɗar ƙasashe da dabarun siyasa, daga Jami’ar Ibadan da ke Jihar Oyo.

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ekitin ya fara aikinsa a matsayin malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Ado-Ekiti, inda ya yi aiki daga 1993 zuwa 1997. Daga baya ya koma aiki a tsohuwar Omega Bank Plc (wadda yanzu ta zama Heritage Bank), inda ya kasance Manajan Baitulmali da Harkokin Kuɗi har zuwa watan Mayu 1999.

Baya ga harkokin gwamnati, Oyebanji yana gudanar da harkokin noma da kasuwancin gona, kuma shi ne Shugaban Kamfanin Con Dois Farms Ltd.

A matsayinsa na fitaccen ɗan kasuwa kuma ma’aikacin gwamnati mai sadaukarwa, ya samu lambobin yabo da dama. Daga ciki akwai Lambar Yabo ta Fitaccen Tsohon Dalibi daga ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Ondo State da kuma Takardar Karramawa daga Ƙungiyar Daliban Kimiyyar Siyasa ta ƙasa (NAPSS).

Ba za a iya rubuta tarihin siyasa da shugabanci a Jihar Ekiti ba tare da ambaton muhimman gudummawar da Abiodun Oyebanji ya bayar ba.

Ya riƙe muƙamai da dama a gwamnati, ciki har da: Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Ekiti kan Harkokin Majalisa  da Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Majalisa (2000–2001) da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan Jihar Ekiti (2001–2003) da kuma Shugaban Hukumar Cibiyar Horar da Ƙasa da Jagoranci ta Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Tarayya (2009–2010).

Sauran su ne: Kwamishinan Ma’aikatar Haɗin Kai da Harkokin Gwamnatoci a Jihar Ekiti (2010–2011) da Shugaban Ofishin Tsare-tsaren Sauyi da Aiwatar da Shirye-shirye na Jihar Ekiti (2011–2013) da Kwamishinan Kasafin Kuɗi, Tsare-tsaren Tattalin Arziki da Aiwatar da Ayyuka na Jihar Ekiti (2013–2014) da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti daga 16 ga Oktoba, 2018.

Oyebanji ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Jihar Ekiti a shekarar 1996, inda ya kasance memba kuma sakataren kwamitin da ya jagoranci ƙirƙirar jihar. Haka kuma ya yi aiki a matsayin Sakataren Asusun Bunƙasa Jihar Ekiti (Ekiti State Development Fund).

Mai Girma Abiodun Abayomi Oyebanji, gwamna jihar Ekiti mai ci a yanzu, shi ne wanda Allah Ya nifa ya saka samun nasara a Zaɓen da a kamala a ranar Asabar, 20 ga watan Yuni 2026 a jihar. Wannann a nuni da cewa zai sake jagorantar ragamar gwamnatin jihar a shekaru huɗu masu zuwa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *