Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadai da kai wani hari da ya yi sanadin kashe wata mata da wasu gungun mutane sukayi a garin Maraban Jos a ranar 21 ga Yuni, 2026
Wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Mandir Hassan, ya fitar ta bayyana cewa an kai wa matar hari ne bisa zargin satar wani yaro.
Sanarwar ta ce domin ceto rayuwarta, jami’an ’yan sanda sun kai ta ofishin ’yan sanda domin kare lafiyarta da kuma gudanar da bincike kan zargin.
- Ƙaruwar marayun sauyin yanayi a ƙauyuka
- Gamayyar masu sa ido ta nuna damuwa game da Zaɓen Gwamnan Ekiti
- Ƙungiyar Matasa Ta Yi Alƙawarin Mara Wa Sojoji Baya, Ta Nemi Ƙarin Haɗin Kai
Sai dai duk da hakan, daga baya wani gungun mutane da yawansu ya kai ɗaruruwa sun mamaye tare da kewaye ofishin ’yan sandan, sun rinjayi jami’an da ke bakin aiki, suka ƙwace matar daga hannun ’yan sanda, suka kashe ta sannan suka ƙone gawarta.
An bayyana cewa matar ’yar asalin Maraban Jos ce.
Rundunar ta bayyana wannan aiki a matsayin dabbanci, laifi mai tsanani da kuma cin zarafi ga doka da oda.
Ta jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon ɗaukar doka a hannunsa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an riga an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da farautar sauran waɗanda suka shiga cikin wannan aika-aika.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yi gargaɗi cewa rundunar ba za ta lamunci kisan gilla, ɗaukar doka a hannu ko kai hare-hare kan ofisoshin ’yan sanda da jami’ansu ba
Ya kuma buƙaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani mutum ko aiki da suke zargi ga jami’an tsaro tare da barin doka tayi aikinta.
Rundunar ta sake tabbatar da aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da adalci bisa tanadin doka.