Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Farfesa Oluwatoyin Temitayo Ogundipe, a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar kula ta ƙasa (NUC).
Farfesa Ogundipe wanda ke da ƙwarewa a fannin ilimi da gudanarwa, zai gaji Olufemi Raphael Aina.
A baya ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor) na University of Lagos sannan kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa (Pro-Chancellor) na Redeemer’s University.
- Bangaren ilimi a Najeriya na fama da karancin kudi – Ministan Ilimi
- An Sauya Sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur ta Kaduna Zuwa jami’ar Shehu Musa Yar’Adua
- Masanin kimiyyar tsirrai William J. ya ziyarci ABU don karfafa cibiyar binciken aikin gona IAR
Farfesa Ogundipe ƙwararren masani ne a fannin Botany (Kimiyyar Tsirrai), kuma mamba ne na wasu manyan ƙungiyoyin masana na duniya, ciki har da Royal Society of Biology.
Ana sa ran zai jagoranci shirye-shiryen da za su inganta tallafin kuɗi ga jami’o’i da ƙara musu damar takara a matakin duniya, da kuma tabbatar da ingancin karatu da gaskiya a harkokin ilimi, domin samar da ɗorewar ci gaba da ingancin tsarin jami’o’in Najeriya.
