Kylian Mbappe ya zura ƙwallaye biyu a wasansa na 100 da ya bugawa Faransa, yayin da suka doke Iraq da ci 3-0 a wasan gasar cin kofin duniya, a filin wasa na Philadelphia.

Kyaftin ɗin na Faransa ya zura ƙwallo a kowane rabin lokaci, kana kuma Ousmane Dembele ma ya zura ƙwallo ɗaya don tabbatar da Faransa ta samu gurbi a zagaye na gaba na gasar.

Da farko, Lionel Messi ya ɗauki hankalin al’umma a kanun labarai a ranar Litinin bayan ya zama wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya da ƙwallaye 18, amma Mbappe yana biye da shi, inda ya kai matsayin Miroslav Klose da ƙwallaye 16.

Mbappe, shi ne ɗan wasa na 10 da ya buga wa tawagar maza ta ƙasar Faransa wasanni 100 kuma ya cimma hakanne yana da shekaru 27 da kwanaki 184.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *