Hukumar tabbatar da dai-daiton mukaman Gwamnatin Tarayya, FCC, ta nua damuwa kan ƙarancin fitowar sabbin mutanen da ke neman aikin soji zuwa wajen tantacewa a Jihar Oyo.

Da yake magana da manema labarai a yayin wani aikin sa ido da aka gudanar a runduna ta 2 ta Mechanised Division, barikin sojoji na Adekunle Fajuyi da ke Ibadan, kwamishinan Hukumar mai wakiltar Jihar Oyo, Prince Ayodeji Abass Aleshinloye, ya koka da abin da ya kira halin ko-in-kula da masu nemar aikin suka nuna.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini, shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a al’umma da su ƙara wayar da kai game da tsarin daukar ma’aikatan, musamman a matakin ƙasa, don tabbatar da cewa matasa ba su rasa damar nan gaba ba.

“Idan aka samar da dama cikin tsarin adalci da dai-daito, masu neman aikin ma dole ne su yi abin da ya dace ta hanyar bayyana kansu da kuma cika dukkan buƙatun da ake bukata,” in ji Alashinloye.

A cewar hukumar, cikin mutane 941 wadanda ke nemar aikin soji a jihar, mutum 472 ne kawai suka halarci wurin tantancewar.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa rashin halartar da aka samu zai iya shafar ƙoƙarin tabbatar da dai-daiton wakilci a ayyukan daukar ma’aikata na tarayya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *