Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta kammala gabatar da shaidunta a shari’ar da take yi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, kan zargin sa ido ba bisa ƙa’ida ba kan hanyoyin sadarwar Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
A zaman kotun tarayya da ke Abuja a yau Talata, mai shari’a Justice Joyce Abdulmalik ta yi watsi da bukatar lauyoyin El-Rufai na sassauta sharuddan belin da aka gindaya masa.
Lauyoyin masu kare El-Rufai sun bayyana cewa sharuddan belin suna da tsauri musamman sharadin da ke buƙatar masu tsaya masa su kasance manyan ma’aikatan gwamnati na mataki 17 masu gidaje a unguwannin Maitama ko Asokoro da ke Abuja, tare da samun takardar shaidar amincewa daga Majalisar Sarakunan gargajiya ta Jihar Kaduna.
- mutum ɗaya ya jikkata yayin da wani abin fashewa ya tashi a Legas
- Ministar Abuja ta nesanta kanta daga zargin naɗin mataimaka bakwai
Sai dai mai shari’a ta ce akwai mutanen da za su iya cika wadannan sharudda, don haka babu dalilin sauya hukuncin da kotun ta yanke a baya.
Bayan yanke hukuncin kan bukatar sassauta sharuddan belin lauyan hukumar tsaro Oluwole Aladedoye, ya sanar da kotu cewa bangaren masu ƙara ya kammala gabatar da hujjojinsa kuma ba zai sake kiran wasu shaidu ba.
Daga nan ne kotun ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 22 ga Satumba, 2026, domin sauraron bukatar da bangaren mai kare El-Rufai zai gabatar ta kuma nemin a sallame shi saboda rashin isassun hujjoji daga masu kara.